Kwamitin da masarautar Kano ta kafa ta tsayar da ranar 26 ga watan maris na wannan shekara a matsayin ranar da kwamitin gyaran aure da zamantakewar iyali zai gudanar da taro, inda zai gayyaci masana don kara wayar da kan al’umma.
Sanarwa ta fito daga bakin wani Malami a tsangayar nazarin sharia ta jami`ar Bayero, DR Usman Shua`ibu Zunnuraini wanda mamba ne a kwamitin ya ce dokar za ta yi duba ne a kan batutuwa biyar da suka shafi auren wuri.
A nasa bangaren wani limamin Masallacin jumu’a, kuma malami a jami`ar Bayero dake Kano Dr Bashir Aliyu Umar, ya bayyana cewa dokar za ta mai da hankali ne kan hanyoyin magance matsalolin da ake fuskanta a tsakanin ma'aurata ta mahangar addini.
Ya bayyana cewa al`ummah za su iya ba da gudumawarsu, kasancewar har yanzu ana aiki a kan dokar.
Ita ma wata da muka zanta da ita Malama Amina Yakubu, ta ce wannan doka zai amfani mata da dama mussamam ma kan baututuwan shi kansa aure da zamantake hada ma matsalolin raino idan aka sami rabuwar aure.
Your browser doesn’t support HTML5