Batun Samun Cutar Shan’inna A Jihar Borno Ba Gaskiya Bane

Rigakafin cutar Shan'inna

Gwamantin jihar Borno ta karyata batun cewa an samu kwayar cutar Shan’inna wadda ake kira Polio a wata unguwa da ake kira Abbagalaram dake cikin garin Maiduguri.

Kwamishinan ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Dakta Haruna Misheliya, shine ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya kira don karyata wannan batu. Yace tun a shekarar 2013 ne aka samu kwayar wannan cuta ta karshe a wani kauye Ajingin dake karamar hukumar Dambuwa a jihar Borno. Sai kuma na watan Yulin 2014 da aka samu a karamar hukumar Sumaila dake jihar Kano.

Tun bayan wancan lokaci dai ba sake samun kwayar cutar ba ko kuma wani yaro dake dauke da ita. Haka kuma an cire kasar Najeriya daga jerin kasashen dake dauke da wannan cuta tun a watan Yulin shekara ta 2015.

Wannan abu dai mai kama da kwayar cutar da aka gano, Dakta Haruna, yace ba cutar Shan’inna bace.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Batun Samun Cutar Shan’inna A Jihar Borno Ba Gaskiya Bane - 3'15"