Gwamnatin Buhari ta bakin shugaban kamfanin mai na Najeriya, NNPC, yacebabu wani shirin kara farashin man fetur yau ko gobe domin gwamnati bata bashi wannan shawara ba.
Babbna daraktan NNP Alhaji Maikanti Baru yace kafofin yada labarai dake ciga da yada labarin jita jita ce kawai su keyi. Ya kira jama'a kada su tada hankalinsu domin gwamnati ta tanadi mai a rumbunta. Kazalika ta kuma tanadi dalar Amurka ma masu shigo da mai domin zage masu wuyar samaun kudaden waje.
Daraktan watsa labarai na kungiyar masu sayarda man fetur Alhaji Yahaya Suleiman yace maganar gwamnati ko 'yan kasuwa sukara kudin mai jita jita ce. Watakila ta samo asali ne daga karin da aka yiwa farashin kerozin ne. Shi ma wannan ya faru ne domin farashinsa ya hau a kasuwar duniya. Amma fetur na nan yadda yake.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5