Batun Inshorar Kiwon Lafiya A Najeriya Ya Sake Tasowa

Sanata Muhammad Ali Ndume

A daidai lokacin da Majalisar Dattawan Najeriya ta kaddamar da kwamitin da zai duba yiwuwar yi wa kundin tsarin mulkin kasar garambawul, maganar bada inshorar lafiya bai daya ta kunno kai.

Ganin cewa tun a shekarar 2005 da gwamnatin tarayyya kasar ta kafa hukumar inshorar lafiya ta tarayya, mutane da dama su na kokawa kan yadda yanayin kiwon lafiya ke fuskantar koma baya, musamman ta hanyar ba al'umma saukin samun magunguna a asibitoci kyauta.

Akan haka ne Muryar Amurka ta tambayi daya daga cikin mambobin kwamitin da zai yiwa kundin tsarin mulkin kasar garambawul, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, ko akwai yiwuwar duba dokar da ta kafa hukumar inshorar?

Sanata Gaya, ya ce "su masu yin dokoki ne, amma kuma aiwatar da dokokin ya rataya ne akan bangaren gwamnati, domin sune suke da kudin yin aiki.

Amma ya ce za a duba ta yadda za a iya kyautatawa mutane domin su samu saukin samun hanyar kiwon lafiya ingantacce.

Sanata mai wakiltar Borno ta kudu, Mohammed Ali Ndume, ya ce yana ganin gwamnatin tarayya za ta iya taka muhimmiyar rawa a wannan fannin, domin akwai kudi a kasa da za a iya ba mutanen Najeriya duka inshorar samun magunguna a asibitoci kyauta.

Ya bada misali da kananan kasashe na Afirka da ke daukar nauyin harkar lafiyar al'ummar su. Saboda haka ya ce idan aka kawo kudurin dokar a Majalisar Dattawa shi zai goyi bayan kudurin.

To sai dai dan majalisar wakilai, Abubakar Hassan Fulata, ya ce abin da kamar wuya, domin ko a kasafin kudin bana ma za a ci bashin Naira tiriliyan biyu kafin a iya aiwatar da shi.

A halin yanzu dai majalisar dattawa ta bukaci a kara yawan asibitoci a fadin kasar baki daya, wanda yin haka zai taimaka wajen cimma burin samar wa mutanen kasar hanyar kiwon lafiya mai dorewa.

A saurari rahoto cikin sauti daga Abuja a Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Batun Inshorar Kiwon Lafiya A Najeriya Ya Sake Tasowa