Jami’an tsaro a Syria sun yi harbi d a nufin tarwatsa masu zanga zanga d a suka fantsama kan tituna bayan jawabind a shugaban kasar Bashar al-Assad ya gabatar ind a yaki janye dokar tabacin kasar.
Shaidun gani da ido a birnin latakia dake kan gabar teku,sunce jami’an tsaro sun harba makamai bayanda daruruwan mutane suka so yin zanga zanga jiya Laraba.kafofin yada labarai a kasashen yammacin Duniya sun ce ‘yan zanga zanga sunyi gangami a birane masu yawa cikin kasar.
A jawabin nasa da kusan mako daya ana dako,Mr.Assad bai nuna wata alamar zai canza dokar ta bacin a jawabinsa na farko ga al’umar kan kasar kan zanga zangogin.
Yace ‘yan kasashen waje da kafofin sadarwa na zamani ne ta haka ake kulla makarkashiyar kifar da gwamnatinsa.Masu zanga zanga sun bukaci da shugaban Kasar ya dake dokar ta bacin na tsawon shekaru hamsin,wacce ta haramtawa ‘yan hamayya shirya ko wani irin gangami.
Amurka tace jawabin na shugaba Assad ya gaza gabatar da sauye sauye da jama’ar Syria suke bukata,kuma hadimansa suke ta yayata cewa zai gabatar cikin jawabin nasa.