Shan miyagun kwayoyi na janyo matsala ga rayuwar bil’adama musamman ta fannin lafiyar su. An sha jefa alamar tambaya akan ko ana iya magance illar da miyagun kwayoyi ke janyowa ga kwakwalwar bil’adama bayan lokaci mai tsawo, ko bayan daina shansu.
Bayan haka ko akwai hanyar inganta lafiyar masu shan kwaya da suka daina sha? Kwararrun gwamnatin Amurka a fannin kimiya na gudanar da bincike, akan kwakwalwar masu shan kwayar da ake kira Opioid da turanci, don ganin ko magungunan da aka yi don hana shan kwayar kamar Methadone, suna yin abinda ya fi rage sha’awar shan kwayar.
Ko magungunan na warkar da kwakwalwar bil’adama da illar shan kwaya ta shafa sosai?
Masana a fannin kimiya sun fayyace cewa magunguna uku, masu suna Methadone, da Buprenorphine da kuma Naltrexone, zasu iya magance abinda kwararru suka kira cutar shan kwayar Opioid.
Masu jinyar shan kwayar da suke shan Methadone ko buprenorphine musamman, suna rage hadarin mutuwa sakamakon shan kwayar ta Opioid da kusan rabi, a cewar wani bincike daga tsangayar kimiyya wanda ya duba yadda za a kawarda abubuwan da ke kawo tsaiko a maganin cutar.
Cutar shan kwayar Opioid na canza yadda kwakwalwa ke aiki, ta hanyar da ko da mutum ya daina shan kwayar yana tattare da hadarin sake komawa mummunar dabi’ar, canje-canjen da masu binciken suka yi imanin cewa suna ragewa, bayan majinyacin ya daina shan kwayar na lokaci mai tsawo mai yawa.