Barcelona Ta Yi Zarra Wajen Sayen Dan Wasa Dani Olmo

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta zarce takwarorinta Manchester United da Chelsea, wajen sayen matashin dan wasan gaba na kulob din Dinamo Zagreb mai suna Dani Olmo.

Barcelona ta sanya kudi har fam miliyan £30m, kimanin yuro €25.6, kwatankwacin dalar Amurka $33.5m, domin ganin ta raba dan wasan da kulob din nasa.

Dani Milo, mai shekaru 21 da haihuwa tuni dai ya bayyana sha'awar canza sheka a wannan watan na Janairu na shekarar 2020, da zarar an bude hada hadar saye da sayar da 'yan wasa.

Sai dai kungiyoyin kwallon kafa na Chelsea da Manchester United, sun jima suna neman dan wasan.

Kungiyar ta Barcelona ta ce tana bukatar dan wasan ne domin ta kara inganta kungiyar, kuma zata sanya shi cikin manyan 'yan wasanta na farko wato ( first team).

A bangaren kungiyar Dinamo Zagreb, ta ce tana bukatar darajar dan wasan ta kai miliyan 40 na yuro (wato fan miliyan 34.1, ko dala miliyan 44.6).