Barcelona Da Valencia Na Tsaka Mai Wuya Akan 'Yan Wasa

Rodrigo Moreno

Barcelona na fargaba game da kokarin da suke yi na neman Rodrigo Moreno, kana tana kokarin tilasta wa kungiyar Valencia ta ba da amsa a yau (Talata), in ji Marca.

Kungiyar na sha'awar samun wanda zai iya maye gurbin Luis Suarez, na tsawon lokaci, tare da dan wasan mai shekaru 33 dan kasar Uruguay wanda zai yi jinyar watanni.

Don haka, sun yanke shawarar matsa lamba akan Rodrigo, wanda ya kasance cikin 'yan gaba-gaba a wadanda suke zawarci.

Sauran kuwa sun hada da dan wasan gaba na Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang, Timo Werner na RB Leipzig da sauran 'yan wasan gaba da dama.

A bayyane yake, shirin Barcelona shine ta ari dan wasa mai shekaru 28, har zuwa karshen kakar wasa tare da tunanin sayan shi na din-din-din a kaka mai zuwa.

Dalilin hanzarin su yanzu shine cewa suna son samun isasshen lokacin, da zimmar zaben nagari kafin a rufe kofar a ranar Juma'a, idan har Valencia ta ki tankawa.

Rodrigo ya shafe shekaru hudu da rabi a Valencia. A wannan kakar yana da kwallaye hudu, kuma ya taimaka aka zura kwallaye 10, sunansa kuwa ya bayyana a wasanni 23 daya buga a duk gasar.