Taron na kwana daya ya hada da masu ruwa da tsaki na bankin da kuma masu ajiya da shi.
Jami'in da ya wakilici shugaban bankin ya zanta da Muryar Amurka akan makasudin taron.
Ismaila Adamu wakilin shugaban bankin mai Muhammad Lawal Islam ya bayyana dalilin taron. Banda jihar Kano jihar Oyo ita ce ta fi kowace jiha hannun jari a bankin amma bankin ya bude rassa a arewa ba tare da bude ko daya ba a kudancin kasar. An san bakin da suna Jais
Bankin kan tura jami'insa ya dinga basu hakuri cewa zasu bude reshe a kudu. Kawo yanzu bankin nada rassa a Maiduguri da Gombe da Yola da Bauchi da Sokoto da Gusau da Katsina da Kaduna da Abuja. Duk gaba daya bankin nada rassa 18.
Ba sai mutum nada kudi ba zai iya bude asusun ajiya sai dai idan nada bukatar takarda ko katin cire kudi.
Bankin baya karbar kudin ruwa kamar yadda bankuna ke yi. Idan mutum ya ranci kudi saboda ya yi wata sana'a ko aiki zasu yi yarjejeniya akan yadda zasu raba ribar tare. Ta wannan hanyar ce bankin ke samun kudi.
Kowa na iya ajiya a bankin ba lallai sai musulmi ba.
Bankin nada jarin nera biliyan 11 da ajiyar mutane kimanin nera biliyan 41.
An fara bankin ne da nera biliyan biyar. Akwai kwastamomi 1038.
Bankin na hulda da Bankin Raya Kasa dake Jiddah Saudiya wanda yake da jarin kashi 8 cikin dari na bankin.Akwai kuma wani bankin musulunci dake kasar Bangladesh wanda ya aiko masu da ma'aikata masu horas dasu. Sun fara hulda da wani bankin kuma na alhazai dake Saudiya wanda zai taimaki alhazan Najeriya.
Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal.
Your browser doesn’t support HTML5