Wanan rahoto na bankin duniya da ke cewa Najeriya ita ce kasa ta 5 a cikin kasashen duniya 10 da suka fi cin bashi bai ba wasu yan kasa mamaki ba duba da cewa wani rahoto makamancin wannan daga Ofishin kdiddiga ta Najeriya na nuni da cewa, kasar ta samu zunzurutun kudi har Naira biliyan 512.25 daga haraji da kasar ke kar6a a wattani uku kachal,wato daga watan Afrilu zuwa watan Yuni na wannan shekara da muke ciki..
Tsohon matamaikin kungiyar ma'aikatan man fetur ta kasa Isa Tijjani, yayi tsokaci akan rahoton da Bankin Duniya ya fitar yana cewa ai kasar ce ta shiga wani hali saboda shi kanshi shugaban kasa mai son cin bashi ne sanan yana hadawa da Majalisar kasa.
Tijjani ya ce abin ya zama na siyasa saboda in majalisa ba ta amince wa Shugaban kasa ya ciwo bashi ba sai abin ya zama gaba tsakanin shi da su. Tijjani ya kara da cewa abin takaici ne a ce Najeriya ta kai har kasa ta biyar a ayarin kasashen da ke yawan cin bashi domin ba a ganin abinda suke yi da kudaden.
Amma ga kwararre a kimiyar tattalin arziki na kasa da kasa Shuaibu Idris Mikati, yana ganin batun kudade da ofishin kididiga ta fatar ana raba shi ne ga bangarorin gwamnatin kasar baki daya, ba gwamnatin tarraiya ce kadai ke amfani da su ba rabawa ake yi tsakanin jihohi da kananan hukumomi.
Shi ma Malami a tsangayar tattalin arziki a Jami'ar Kashere ta Jihar Gombe Dokta Isa Abdullahi yayi tsokaci akan batun yana cewa komin yawan kudaden da ake samu a kasar dole ne a ciwo bashi, saboda akwai wasu cibiyoyi na dimokradiya wadanda suka zama kafafe na cinye kudaden da ake samu. Abdullahi ya bada misali da yan majalisu da gwamnoni 37 da Majalisun jihohin gaba daya suna cikin bangarorin da ke cinye kudaden, saboda haka alamu ne da ke nuni da cewa gudanar da dimokradiya harka ce mai tsada sosai.
Bankin duniya ya ce basussukan Najeriya tare da cibiyar hada-hadar kudade ta kasa ya kai dalar Amurka biliyan 11.7 kwatankwacin Naira Triliyan 4.816.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5