Bankin Duniya (World Bank) Ya Sake Sukar Tsarin Canjin Kudi Na Babban Bankin Najeriya

CBN

Bankin Duniya ( World Bank) ya sake sukar salon tsarin canjin Kudi na Babban Bankin Najeriya a daidai lokacin da ra'ayoyi tsakanin masana tattalin arziki da manazarta suka banbanta akan yadda ake sayar da dala daya wanda a yanzu ya kama Naira 760 a kasuwar bayan fage a maimakon Naira 445.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na yanar gizo, Bankin Duniya ( World Bank) ya bayyana cewa tsarin tafiyar da canjin kudi na Babban Bankin Najeriya CBN ya jawo ma kasar asarar zunzurutun kudi har dalar Amurka biliyan 144.1 daga shekarar 2017 zuwa kwata na farko na shekarar 2021.

Rahoton ya nuna cewa Bankin Duniya da ma Asusun Lamuni na Duniya sun mayar da hankali sosai akan yadda Babban Bankin Najeriya ke tafiyar da manufofin canji a kasar inda suka bada shawarar yin canji a hukumance. Amma Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya dage cewa tsarin kula da ruwa a halin yanzu shi ne mafi a'ala a kasar.

To sai dai wani kwararre a fannin tattalin arziki, Abubakar Ali, yana ganin duk ba a nan gizon ke saka ba, saboda a Najeriya babu masana'antu da ke sarrafa abubuwa da za a sayar a kasashen waje domin samun kudaden kasashen wajen.

Ali ya ce wannan ne babban matsala kuma matukar ba farfado da masana'antun aka yi ba, darajar Naira ba za ta farfado a yanzu ba.

Shi kuwa manazarci a fannin tattalin arziki da cigaban kasa kuma malami a Jami'ar Tarayya ta Kashere a Jihar Gombe, Dokta Isa Abdullahi, na ganin akwai abin dubawa a salon canjin kudi da kasar ke amfani da shi.

Abdullahi ya ce an rasa yawan kudaden ne saboda walau an yi amfani da su a wauraren kwangila ko kuma wasu ayyuka na cigaban kasa amma kuma ba a bi diddigin yadda aka kashe su ba, shi ya sa babu bayaninsu.

Amma daya daga cikin manyan masu canji a Birnin Tarayya, Umar Garkuwa, ya bayana ra'ayinsa akan faduwar darajar Naira inda ya ce ai daga bankunan kasar ne ake fitar da dala ba daga ko ina ba.

Umar yace wannan kawai ana nade tabarmar kunya ne da hauka kawai.

Amma a wata hira da yayi da Muryar Amurka a kwanakin baya, Darektan Kudi na Babban Bankin Najeriya, Ahmed Bello Umar, ya ce duk abin da CBN ya yi a harkar hadahadar Kudi a kasar ba a yi shi domin a musguna wa kowa ba.

Umar ya ce in aka kammala canjin da ake yi a tsarin, komi zai daidaita nan gaba kadan.

Abin jira a gani shi ne irin sauyin da CBN zai yi wajen sake farfado da darajar Naira da a yanzu haka ake sayar da Naira 760 kan dala guda a kasuwar bayan fage amma kuma ana sayar da dala kan Naira 445 a bisa ka'ida.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

CBN CASHLESS POLICY AFFECTS EXCHANGE RATE OF THE NAIRA --REPORT.mp3