Bankin duniya tare da sa hannun Gwamnatin jihar Neja sun kaddamar da aikin samar da sababbabin hanyoyin yankuna karkara da yakai tsawon kilomitoci dari hudu da ukku a wadansu kauyuka guda goma sha biyu na jihar Neja.
Jagoran shirin samar da hanyoyin yankunan karkara na Najeriya wanda ake kira da RAM. Eng Uban Doma Ularamu, yace ana sa rai za’a kaddamar da wannan aikin ne zuwa karshen shekata ta 2019, inda Bankin Duniya zai kashe Dalar Amurka Milyan 60 wajan gyara Hanyoyin karkara a jihar Neja,
Bayan nan kuma Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya kaddamar da wani aikin sabuwar hanyar da Gwamnati ta yi daga kamfanin bangi zuwa Bobi.
Saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari
Your browser doesn’t support HTML5