WASHINGTON D.C —
Bankin tallafawa ci gaban kasashen Afirka AFDB ya bayyana cewa zai shiga sahun wasu bankunan duniya domin samar da dala bililiyan 20 ga shirin iskar gas na kamfanin LNG a Mozambique.
Bankin ya ce ya kammala shirin bayar da na shi kason talaffi da bashin dala miliyan 400.
Shirin na iskar gas na LNG a Mozambique wanda ake sa ran zai ci dala biliyan ashirin shi ne jarin kasar waje ma fi girma kawo yanzu a nahiyar Afirka.
Aikin zai kunshi har da jiragen kasa masu tsawo guda biyu da za su rinka safarar tan miliyan 13 na iskar gas a kowace shekara.