Bangarorin dake fafatawa da juna a Yemen sun amince su yi sulhu

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Yemen, Ismail Ould Cheikh Ahmed

A kasar Yemen, bangarorin dake cikin rikicin da akeyi sun amince da matakan kawo karshen fada da kuma wani sabon zaman sulhu da aka shirya a watan gobe.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya, MDD na musamman a Yeman, Ismail Ould Cheikh Ahmed, ya fada a jiya Laraba cewa, yarjejeniyar zata fara aiki ranar 10 ga watan Afrilu. An kuma shirya zaman tattaunawar da bangarorin gaba da gaba ranar 18 ga watan Afrilu a Kuwait.

Chikh Ahmed ya fadawa manema labarai a birnin New York, cewa “manufar tattaunawar shine a samar da wata jarjejeniya, wadda zata kawo karshen fadan da akeyi da kuma samo hanyar sasantawa a siyasance.” Ya kuma ce zaman zai zamanto ne akan shawarwarin kwamitin sultu na MDD, wanda yake kira da a sasanta rikicin wanda ya kai tsawon shekara a siyasance.

Sama da mutane Dubu 6 ne suka rasa rayukansu tun lokacin da kasar Saudiyya ta fara jagorantar kai hare hare ta sama a watan Maris din shekarar da ta gabata, yayin da Saudin ke goyon bayan shugaban kasa Abd Rabbu Mansour Hadi, wanda ya arce zuwa Riyadh bayan da yan tawayen Houthi da Iran ke marawa baya sun kwace babban birnin Sanaa a watan Satumbar shekara ta 2014.

Wannan tattaunawar dai zata mayar da hankali kan wasu muhimman abubuwa biyar. Wanda suka hada da samar da hukumomin wucin gadi akan tsaro, ma’aikatu, tattaunawar siyasa da kwamitin musamman akan wadanda ake tsare da su.