Bangaren man Nijeriya na fama da sata

  • Ibrahim Garba

Masu zanga-zangar karin farashin mai a Nijeriya

Wani katafaren kamfanin mai ya ce ya ce bangaren albarkatun man

Wani katafaren kamfanin mai ya ce ya ce bangaren albarkatun man Nijeriya ya gaza kasa da abinda karfinsa zai iya cimma saboda sata da mabarnatan hukumomi.

Ian Craig, Daraktan kamfanin Royal Dutch Shell na Sashen Afirka kudu da Sahara, ya ce Nijeriya na iya samar da gangar mai miliyan 4 a rana. To amman Craig ya fadi a wani taron bita a yau Talata dinnan a Abuja cewa barayi na sace ganguna 150’000 a rana ta lodawa a sace ko kuma fasa bututan mai su sace shi.

Craig ya kuma zargi kamfanin man Nijeriya NNPC - wanda ke hulda da dukkannin kamfanonin man kasashen waje – da kin daukar nauyin shirye-shiryen da su ka kamata.

Shell ne kamfanin mai mafi girma a Nijeriya, wadda ita ce kasar da ta fi arzikin mai a Afirka, a yanzu ta na samar da gangar mai kimanin 2.4 a rana.

Yawan man da ake samarwa ya yi kasa sosai kafin 2009, bayan da aka bullo da shirin yin afuwa ga ‘yan bindigar Naija-Delta wadanda kan auna kayan aiki, da bututan mai da kuma ma’aikata a yankin na Naija-Delta mai arzikin man fetur.

&nbsp

Aika Sharhinka