Daga aikin hajjin bana a Najeriya kudin kujerar bai daya zai kama Naira miliyan daya da dubu dari biyar banda kudin guzuri na dala dari takwas ko Naira 244,000.
Wannan farashin ya biyo bayan tsadar dalar Amurka ne da aka samu a Najeriya. Bara an sayarwa alhazai dalar akan Naira 197 to amma a wannan shekarar zata kama Naira 305 ne kowace dala daya.
Wadannan bayanan sun fito fili ne bayan gayyatar da kungiyar gwamnoni ta yiwa shugaban hukumar alhazan Barrister Abdullahi Mukhtar Muhammad wanda yayi bayani filla filla.
Shugaban kungiyar gwamnoni Abdulaziz Yari yana mai cewa sun kira shugaban hukumar ta kasa domin ya basu tsarin ayyukan hajjin bana tare da farashin kujerar zuwa hajjin ganin cewa dala tayi tsada bana.Yace ana harsashen a sayar masu da dala akan Naira 305 maimakon 197 da aka sayar masu bara.
Dangane da masu daukan alhazai a wannan shekarar Gwamna Yari yace suna samun takurawa daga hukumomin Saudiya saboda sun hakikance dole ne a bar kamfanonin kasarsu su kwashe kashi hamsin cikin dari na duk alhazan da zasu tashi daga Najeriya zuwa Saudiyan. Yace 'yan Najeriya masu sana'ar zasu takura.
A nashi bangaren shugaban hukumar alhazan Barrister Abdullahi Muhammad yace duk wanda Allah ya baiwa damar zuwa aikin hajjin bana zai ga inganci a tsarin motocin hawa da wurin kwana da abinci da datsarin kiwon lafiya da harkokin tsaro.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5