Bana Babu Turmitsitsi A Wajen Jifan Shaidan A Saudiya

Aikin hajjin bana

Ba kamar yadda ta faru ba bara a wajen jifan Shaidan lokacin aikin hajji inda bubban mutane suka rasa rayukansu, bana an yi jifan cikin tsanaki ba tare da wani turmitsitsi ba

Kimanin alhazai miliyan biyu daga kasashe daban daban suka kammala hawan Arfa tare da jifan Shaidan a kasar Saudiya ba tare da samun wata matsala ba kamar kamar can baya.

Gudun kaucewa abun da ya faru lakcin aikin hajjin bara kasar ta Saudiya ta dauki tsauraran matakan tsaro domin ganin an gudanar da aikin hajjin cikin nasara.

Idan ba'a manta ba bara an yi asarar alhazai da dama a wajen jifar Shaidan sakamakon turmitsitsin da ya auku. ida mutane suka dinga turereniya.

Alhazai da suka taru lokacin Arafa yau

Kasar Kamaru mai alhazai dubu ukku da dari bakwai da suka yi aikin hajjin bana tace ta yabawa kasar Saudiya kan yadda aikin ya gudana. Mataimakin amir hajjin kasar yace basu samu wata matsala ba.

Shi ma Amir hajjin Najeriya Etsu Nupe Alhaji Yahaya Abubakar ya jagoranta yace sun gamsu da yadda aikin ya gudana. Mataimakinsa sarkin Dass Alhaji Bilyaminu Usman ya tabbatar da hakan.