Bam Ya Kashe Mutane Bakwai Kusa da Fadar Shugaban Somalia

Sojan kasar Somalia kusa da inda bam ya tarwatse

Wata motar ‘yan kunar bakin wake dauke da bam ta tarwatse a kusa da fadar shugaban kasa a Mogadishu babban birnin kasar Somalia, ta kashe mutane akalla bakwai.

Jami’an asibiti sun ce akalla mutane 21 sun jikkata a harin da ya auku bayan karfe 6 na yammacin jiya Litinin.

Likitar asibitin Medina, asibiti mafi girma a Mogadishu ta fadawa sashen Somali na Muryar Amurka cewa fiye da rabin wadanda suka ji raunin suna cikin mawuyacin hali.

Dan kunar bakin waken bam din ya gwabza motar ne a shingen binciken da ke kusa da fadar ta shugaban kasa, inda gidaje da ofisoshin shugaban kasa da Firaminista suke.

Jami’an tsaro sun ce a lokacin da abin ya faru, tawagar Majalisar Dinkin Duniya dda wakilin majalisar na musamman Nick Kay, suna gab da barin fadar shugaban kasar lamarin ya faru.

Ba’a sani ba koshi ne aka so a hallaka amma babu abun da ya sameshi. Amma mutane biyu daga jami’an tsaronsa sun mutu.

Kay yayi alla wadai da harin ta’addanci da yace na rashin imani ne, sannan da son yin karan tsaye ga ci gaban siyasar kasar.

Mahukuntan Somali’a da na Majalisar Dinkin Duniya dai sun taru ne don tattauna yadda za’a tsara mika mulki a Somalia a shekarar 2016 idan Allah ya kaimu.

Kungiyar Al-Shabaab dai ta dauki alhakin kai harin, sannan tun a shekarar 2006 suke ta kokarin hambarar da gwamnatin Somalia don kafa shari’ar Musulunci.