Bam Ya Hallaka Mutane 4 A Damaturu

  • Ibrahim Garba

Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau

Yayin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke kokarin samun taimakon Amurka wajen yaki da Boko Haram, kungiyar ta kai wani hari a Damaturu, inda ta hallaka mutane 4, na bayabayan nan a jerin hare-haren da kungiyar ke kai wa

Bam ya tashi a wani wurin duba ababen hawa a jahar Yobe, ya hallaka mutane akalla hudu banda wadanda ya raunata.

Wannan harin ya zo ne kwana guda bayan sanarwar da Hafsan sojojin kasar Manjo Janar Tukur Burutai ya bayar na canza ma rundunar suna daga Operation Zaman Lafiya zuwa Operation Lafiya Dole.

Ana ganin harin, wanda aka kai inda ‘yansanda ke duba ababen hawa daf da shiga garin Damaturu, an auna shi ne kan ‘yan sandan. To amma harin ya shafi ‘yansandan da maharan da kuma wasu da ke daura da wurin.

Wani ganau ya gaya ma wakilinmu wanda ya aiko da rahoton, Haruna Dauda cewa harin ya auku daura da “depo” din NNPC kuma ya tabbatar da mutuwar mutanen y ace a mota maharani su k azo da bam din kuma sun tayar da shi ne bayan da aka tsaida su don bincike

Your browser doesn’t support HTML5

BAM YA HALLAKA MUTANE 4 A DAMATURU - 2'01''