Tsohon Ministan Birnin Tarayyar Najeriya Abuja, Sanata Bala Muhammad Duguri (Kauran Bauchi), wanda ya yi takarar gwamnan jahar Bauchi karkashin jam’iyyar PDP, shi ne Hukumar Zaben Najeriya mai Zaman kanta (INEC) ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jahar Bauchi, wanda ya gamu da kwan gaba kwan baya, har da matakin kotu, kafin takaddama da sauran matsalolin su ka zo karshe, har aka sanar da sakamakon zaben cikin tsakiyar daren jiya.
Zababben gwamnan, Sanata Bala Muhammed, ya sami kuri’u dubu 515,113, sai kuma wanda ya zo na biyu, wato gwamna mai barin gado, Muhammed Abdullahi Abubakar na jam’iyyar APC, ya sami kuri’u dubu 500,625.
Da ya ke bayyana sakamakon zaben, babban jami’in sanar da sakamakon zaben gwamnan ya ce: Shi farfesa Kyari Muhammed ya na tabbatarwa cewa shi ne babban mai sanarwar sakamakon zaben gwamna na jihar Bauchi na shekarar 2019 da aka gudanar, kuma Bala Abdulkadir Muhammed na jam’iyyar PDP, bisa cimma bukatar doka, kuma da yak e ya sami kuri’u mafiya rinjaye, shine ya lashe zaben.
Wakilin jam’iyar PDP a wajen bayyana sakamakon zaben ya bayyana murnar da jam’iyyar ta su ta yi. Wani mai sa ido a harkar zabe ya bayyana cewa an gudanar da zaben cikin nasara, babu tashin hankali. Daga bisani zababben gwamana mai jiran gado Senata Bala Muhammed Duguri (Kauran Bauchi), ya gana da manema labarai don gode wa al’ummar jahar Bauchi game da zabansa da su ka yi. Masu kade kade da raye raye su ma sun cashe.
Ga Abdulwahab Muhammad da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5