Bakin Haure Sun Ce Su Na Fuskantar Ukuba A Libiya

Abune mai wuyar gaske a iya kimanta munmunan halin da bakin haure ke ciki a kasar Libiya.

Kan hanyar zuwa Libiya mutum zai ci karo da fyade, kisa, garkuwa kai babu wani abu da mutum ba zai gani ba. Ko kamun shiga cikin wannan mawuyacin halin, wadannan mutanen sun gujewa yake-yake, harin kungiyoyin miyagu, kai harma da talauci, sun bar gidajen su don suna bukatar hakan.

Libiya ita hanya ce mafi sauki don zuwa kasashen Turai, kuma mafi akasarin matafiyan suna sa ran zasu kaiga cinema burin su.

Amma a karshe su kan fuskanci zaman kurkuku, kadaici, yaki, harma da matsanancin talauci, a cewar matafiyan tsoro kuwa abune da ba’a guje mishi.