Shugaban hukumar a jihar Neja Mr. Ezekiel Kaura yace wadanda aka cafken sun fito ne daga kasashen Nijar, Chadi da Mali.
Ta bakin Mr. Kaura yace mutanen da suka cafke sun kai dari biyu da goma sha daya. Yace dukansu an mayar da su kasashensu.
To saidai mayarda mutanen a daidai lokacin da babban zaben Najeriya ke karatowa ya bar baya da kura. Tuni jam'iyyar adawa ta APC a jihar Neja tace magoya bayanta ne a ka kwashe da zargin cewa bakin haure ne.
Mr Jonathan Batsa kakakin jam'iyyar APC yace batun ba haka yake ba. Hukumar shige da fice bata fito ta fadawa 'yan Najeriya gaskiya ba. Gwamnati ce take anfani da hukumar take kwashe mutane da nufin ragewa jam'iyyarsu kuri'u domin mutanen ba zasu zabi PDP ba. Mr Batsa ya hakikance sabili da zabe aka yi. Yace menene ya sa basu yi hakan ba tuntuni.
To saidai kwantrolan hukumar na jihar Neja yace kamen da suka yi bashi da alaka da siyasa. Yace babu abun da ya hadasu da siyasa. Aikinsu ne suka yi.
Jami'in yada labarai na PDP Alhaji Hassan Saba ya mayarda martani. Yace maganar cewa da hannun PDP cikin kamen bata ma taso ba domin ba su suka sa a yi ba ba su ne kuma hukumar shige da fice ba. Idan hukumar tayi daidai kasar ta taimaka. Idan kuma bata yi daidai ba za'a tambayi ma'aikatar.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5