BAKI MAI YANKA WUYA

Murtala Faruk Sanyinna

Yayin da matsalar tsaro ke ci gaba da ta’azzara a yankin Arewacin Najeriya, manazarta na bayyana matakin da gwamnatin kasar ke daukawa a matsayin wasan kwaikwayo. Wasu kwangilolin samar da ruwa da gwamnatin jihar Sokoto ta ce ta bayar sun ta da kura tare da janyo cece-kuce.

A daidai lokacin da ake ci gaba da jimamin rasuwar Sarkin Gobir na Sabon Birni a jihar Sokoto a hannun ‘yan bindigar da suka sace shi, wasu al’amura sun biyo baya da masu fashin baki ke ganin sun kara bayyana matakin koli na tabarbarewar sha’anin tsaron a fadin Najeriya.

Ko baya ga bidiyon martanin kasurgumin dan bindiga Bello Turji kan rasuwar ta Sarkin Gobir, akwai kuma wasu bidiyoyi na kisan jama’a da sauran ayukan ‘yan bindigar daban-daban, wadanda kuma ‘yan bindigar ne suka saka su a duniya.

Wanda ya fi jan hankalin jama’a shi ne yadda aka ga Turji da yaransa suna tsallen murna kan wasu tankokin yaki na soji da suka ce sun kwace bayan fatattakar sojojin, wadanda daga bisani suka cinna musu wuta.

Tuni dai al’umma musamman a shafukan sada zumunta suka yi ta baiwa wannan al’amari fassarori da dama, abin da ke nan ya sa Rundunar tsaron Najeriya ta bakin Group Captain Ibrahim Ali Bukar, ta yi bayani kan rahoton bincike dangane da wannan lamari.

To wannan al’amari ya haifar da shakku kan matakan da gwamnatin kasar ta ce tana dauka a yaki da ‘yan ta da kayar baya, musamman na baya-bayan nan da aka ga karamin ministan tsaron kasar Bello Matawalle, tare da manyan hafsoshin tsaron kasar, da suna sun tare a Sokoto domin kawo karshen ‘yan bindiga, lamarin da wasu ke gani tamkar wani wasan kwaikwayo ne da aka tsara.

Shugaban kungiyar Rundunar Adalci kuma dan asalin yankin Sokoto ta Gabas, Basharu Altine Guiyawa Isa, ya dade yana bibiyar yanayin tsaron yankin.

Shi kuwa kwararre a fannin sha’anin tsaro da binciken sirri, Dr. Yahuza Ahmad Getso, cewa yayi wannan yanayi ya bijiro da tambayoyi da dama, da ya wajaba akan gwamnati ta amsawa ‘yan Najeriya.

To sai dai Kanal Muhammad Dole, tsohon babban jami’in soji da yayi aiki a rundunar kawancen tsaron yankin tafkin Chadi, ya ce wannan matakin ya yi daidai.

Amma duk da haka, Wing Commander Musa Isah Salman mai murabus, yana ganin matakin da gwamnati ta dauka na tarewa a Sokoto, a zaman abin dariya.

A saurari shirin tare da Murtala F. Sanyinna:

Your browser doesn’t support HTML5

9/04/2024 - BAKI MAI YANKA WUYA.mp3