A yayin da al’umomin yankin na zargin shugabanin yankin da tunzura matasa, wata kungiya mai fafutukar kare yankin na Niger Delta, mai suna Niger Delta Alliance, dake karkashin Madam Rita Lori, wata mai fafutukar kare yankin na Niger Delta, ta bayana matakin da gwamnatin Najeriyar tace zata dauka na dawo da biyan kudaden zaman kasha wando ga matasan tsagerun Niger Delta, da cewa bazai taimaka wajan kawo karshen ta’addanci da zagun kasa ga tattalin arzikin Najeriya ba.
Tace sai idan shugabanin yankin sun daina amfani da matasa a aiyukan banga da makamantasu wajan biyan bukatunsu da na siyasa.
Madam Rita Lori, tace shugabanin yankin sune suke lallata matasa ta maida su karnukan farauta wajan riklicin siyasa da makamantansu amma don zuwa neman tallafi daga shugaba Muhammadu Buhari, domin ciyar da yanking aba ba zai tabbata ba sai an magance wannan matsalar baki daya.
Ta kara da cewa tana daya daga cikin jagororin yankin dake gudanar da zanga zanga da kuma sadaukar da rayukan mu domin samun ‘yancin yankinn amma wasu tsiraru masu hana ruwa gudu da kuma rashin kishi na ci gaba da amfani da matasan yankin domin cimma bukatunsu na siyasa.
A wani bangaren gwamnatin jihar River, ta bakin kwamishinanta na yada labarai Mr. Tam George, yace basu goyon bayan matakin gwamnatin Najeriya, na baiwa matasa yankin kudaden karshen wata da nufin kawo karshen aiyukan zagon kasa a yankin na Niger Delta, a maimakon hakan gwamnatin jihar ta dukufa ne wajan koyawa matasa sana’oi, domin su kasance masu dogaro da kai.
Your browser doesn’t support HTML5