ABUJA, NIGERIA- Wannan batu na kama matashin mai suna Muhammad Aminu tare da gurfanar da shi a gaban kulliya ya haifar da muhawara mai zafi a kafofin yada labarai da na sada zumunta a Najeriya inda da dama ke gannin an wuce gona da iri wajen daukar hukunci lakada masa duka daga bisani kotu ta ba da umarnin a tura shi gidan yari kafin a ci gaba da yi masa shari'a.
Tuni dai kungiyoyin kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa a Najeriya irinsu Amnesty International su ka yi Allah-wadai da matakin kama Muhammad tare da zargin an take masa hakkinsa na bil adama.
“Na daya dai an ce wannan laifin a Jigawa aka yi, sannan aka aika jami’an tsaro suka kama yaron suka je su ka kulle shi aka rika jibgar sa. Wannan ya keta dokar kasa ya keta dokar bil Adama”…. A cewar Auwal Musa Rafsanjani shugaban gudanarwa na kungiyar Amnesty International.
Bayanai na nuni da cewa, uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ce ta bai wa jami'an tsaro umarnin dauko mata Aminu daga jihar Jigawa bayan ya wallafa wasu kalamai a kanta na zargin ta yi rub da ciki da kudin jama’a kalaman da ba su mata dadi ba.
Da ta ke tsokaci kan lamarin, Hajiya Naja'atu Mohammed Kwamishiniya a Hukumar 'Yan sandan Kasar ta ce, ya kamata a kama 'uwargidan shugaban kasar saboda ta keta doka ita kanta.
"Ta karya doka saboda ta dauki doka a hannunta idan ma yaron ko yaran nan sun mata laifi doka ainda ta ce komai muna da shi a tsare, doka abunda tace shine a kai kara"... In ji Hajiya Naja'atu Mohammed. Ta kuma ce, ya kamata a kama 'uwargidan shugaban kasar saboda ta keta doka ita kanta.
Yayin da wasu ke sukar wannan mataki na hukunta dalibin wasu na ganin hakan ya yi daidai don ya zama izina ga sauran matasa da ke shagala tare da cin zarafin mutane a kafofin sada zumunta.
“Ina goyan baya bama yaron nan ba duk mutumin da zai fito Soshiya midiya ba bisa hujja ba, ba bisa kana da shaida ba sai don dan radin kan ka aka ci mutuncin wani, ina goyon baya dari bisa dari. Ba dana ba, ko ni ne na yi doka ta hau kaina”… A cewar Shugaban Kungiyar Matasan yankin Arewa ta gabas Abdulrahman Buba kwacham.
Har izuwa lokacin hada wannan rahoto, uwargidan shugaban kasa da jami’an tsaro ba su ce uffan kan wannan batu ba na Muhammad Aminu dalibi da ke zangon shekara ta karshe a jami’a wanda ke shirin rubuta jarabawarsa ta karshe a ranar 5 ga watan Disamba.
Saurari cikakkan rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5