Badakalar Daukar Matasa Dari Biyu Aiki Na Gwamnatin Tarayya

Yemi Oshinbajo

Tun lokacin da ofishin mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Oshinbajo, ya fitar da sunayen matasa dari biyu daga cikin matasa dubu dari biyar da gwamnatin tarayyar Najeriya, ta tara zata baiwa aiyukan yi aka fara samun ce ce ku ce, dagane da manufofi da hanyoyin da aka bi sun nuna akwai matsalar kabilanci da rashin bin ka’ida.

Hakkan ya fito fili ne ganin yadda aka dora sunayen da ake zaton cewar ba sunayen ‘yan wadanna jihohi bane kamar yadda aka ganin a sunayen ‘yan arewacin Najeriya.

Wani tsohon Minista, a Najeriya, kuma jigo a jam’iyyar APC, Alhaji Umaru Dambo, yace ‘yan kasa nada hujja suyi koke koke ganin irin sunayen da aka buga a jaridu, wanda bai dace da sunayen ainihin ‘yan jihohin da sunayen ke wakilta ba.

Hajiya Maryam Uwais, babbar jami’ar, dake kula da wannan bangare na tallafawa al’uma da kuma samarda aiyukan yi ga matasa, tace yanzu za’a gyara domin wannan sunayen dubu dari biyu da aka fitar ya nuna inda matsalar take.

Your browser doesn’t support HTML5

Badakalar Daukar Matasa Dari Biyu Aiki Na Gwamnatin Tarayya - 4'42"