Mafi akasarin al’umah na da yakinin cewar sana’ar saida turare, sana’ar mazace ana cikin haka sai ga wata baiwar Allah da take wannan sana’ar kuma tasa mu alkhairi acikin sana’ar. Wannan malamar sunanta Baraka Salisu Albdullahi, wadda take dalibace a jami’a.
Kuma tace wannan sana’ar tata tana samun abubuwan da take taimaka ma kanta batare da ta tambayi iyayen ta wani abu ba, ta fara wannan sana’ar kamar wasa takan sayi wannan turare daga Kano sai ta tafi da su Kaduna, wanda ake zuwa gida ana siye. Kuma mutane sun santa da wannan sana’ar kuma maza da mata na zuwa don siyan wannan kala-kalan turaruka da take siyarwa.
Kuma tayi kira ga mata suma su shiga wannan sana’ar don kuwa ana samun alkhairi musamman ma mata masu iyalai, don ta wannan hanyar zasu iya taimaka ma iyalan su batare da sun jira masu gidajen su ba. A sanadiyar wannan sana’ar tata har takan biya makanta kudin makaranta da ma wasu abubuwan rayuwa na yau da kulun.