Babu Wata Hujjar Kasa Magance Matsalar Tsaro - Buratai

Babban Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai

Babban hafsan sojojjin Najeriya, laftanal janar Tukur Yusuf Buratai ya gargadi dakaru na musamman da aka jibge a jihar Katsina da su zage damtse domin magance matsalolin tsaro.

A cewar Buratai dai, "ba ku da wani dalili na kin magance matsalar tsaron a jihar."

Jaridar Punch a Najeriya, ta ruwaito cewa Buratai ya fadi hakan ne a jiya Lahadi yayin wata tattaunawa ta musamman da ya yi da wasu manyan shugabbanin tsaro.

Ya kuma yi musu kashedi kan mu'ammala da wadanda ke da miyagun manufofi, a yayin da yayi musu tunin cewa biyayyarsu tana ga Najeriya da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

"Baku da wata hujjar kasa cika wannan aikin na ku. Ku kwararru ne. Fatanmu shi ne matsalar rashin tsaro ta kawo karshe nan ba da dadewa ba."

Babban Hafsan Sojojin Najeria Janar Tukur Yusuf Burutai Tare Da Wasu Sojoji a Sambisa

Hakan dai na zuwa a daidai lokacin da rundunar sojin da gwamnatin Najeriya ke ci gaba da fuskantar suka daga bangarori da dama a kasar, saboda yadda tsaro ke kara tabarbarewa, musamman ma a arewacin Najeriya.

A cikin watan da ya gabata ne Shugaba Buhari ya umurci shugabbanin tsaro da su kai farmaki na musamman a jihar Katsina, wacce ta kasance daya daga cikin jihohin da 'yan bindiga suka fi kai wa hare-hare.