Babu Wanda Zai Tsira a Wannan Gwamnatin Matukar Yayi Zarmiya -Magoya Bayan Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammad Buhari

Tunda shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya dakatar da sakataren gwamnati da shugaban hukumar tara bayanan siri ba tare da wani mataki mai tsauri ba magoya bayan shugaban suka ce a wannan gwamnatin babu wanda zai tsira matuka yayi zarmiya

Dan APC Yau Ciroma yace kodayake tafiyar tana tanga-tanga shugaban yana nan kan bakarsa muddin ya tabbatar wanda yake aiki dashi barawo ne zai kawar dashi ya fuskanci sharia.

Yace shi shugaban kasa dole ne ya sanya rigar soja tare da takalmin karfe ya yaki cin hanci da rashawa.

To saidai PDP na adawa da kafa kwamitin bincike da mutanen gwamnati maimakon a sa wasu dake zaman kansu. Tana ganin ba za'a yi adalci ba.

Barrister Abdullahi Jalo wanda yayi magana a madadin jam'iyyarsa ta bangaren Ahmed Makarfi yace ga mutum an sameshi da sata kana an nada aminansa wai su bincikeshi, yana cewa tamkar rena hankali ne.

Amma dan PRP Alhassan Kakale yayi na'am da matakin na gwamnati. Dakatar da jami'an biyu ya nunawa duniya cewa ko dan cikinsa aka sameshi da yin zarmiya zai hukumtashi, inji Kakale.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Babu Wanda Zai Tsira a Wannan Gwamnatin Matukar Yayi Zarmiya -Magoya Bayan Buhari - 6' 10"