Duk wani mai rike da mukami na saurata a daukacin jihar Zamfara, idan bai kawo karshen kashe-kashe da dauke-dauke da ake yi a yankunan shi ba, babu shakka zan tsige shi cikin kankanin lokaci, injin Gwamnan jihar Zamfara ke nan Alh. Bello Matawalle.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata zantawa da ya yi da Muryar Amurka inda ya ce suna da rahotanni da suka tabbatar masu cewar gwamnatin da ta gabata ta daukin 'yan saka kai a kowacce karamar hukuma, karkashin jagorancin sarakunan yankunan.
Don haka sarakunan sun san wadannan mutanen, idan aka yi wani abu a yankunan, ya kamata a ce sun san wadanda suka aikata, wannan ya sa muka fito da shirin tsige duk wani da bai kawo karshen wannan matsalar ba.
Ya kara da cewa, ko a 'yan makonnin baya sun je wata karamar hukuma inda mutanen yankin suka nemi a bar su su kashe sarkinsu, don suna gananin cewar yana da hannu akan irin rashin adalci da ake yi wa makiyaya a yankin, na kwace musu dukiyoyinsu.
"Ina kira da jama'ar jihar mu ta Zamfara da ya kamata mu hada kai da hannu waje daya don kawo karshen rashin zaman lafiya da muke fama da shi a jihar, gwamnati ta, a shirye take ta karbi duk wata shawara da mai son ci gaban jiha zai kawo."
A saurari cikakkiyar tattaunawar Yusuf Aliyu Harande da gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle.
Your browser doesn’t support HTML5