Babu Wanda Ya Can-Canci Ballon d'Or Kamar Samuel Eto'o

Samuel Eto'o

Tsohon kocin Manchester United, Chelsea da kuma Real Madrid, Jose Mourinho, yace yayi imanin tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa na Kamaru, Samuel Eto'o ya cancanci ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya, ko da sau daya ne a lokacin da ya ke fafata wasa kafin ya ajiye takalman wasa.

A ranar 7 ga watan Satumbar shekara 2019 Samuel Eto'o, mai shekaru 38 da haihuwa wanda ya taba buga wasa wa Barcelona, Real Madrid, Inter Milan da kuma Mallorca, ya ajiye takalman buga wasansa bayan ya shafe shekaru 22 yana taka leda.

Inda ya samu nasarar lashe kofin kasashen Afirka sau biyu da kuma na zakarun turai Champions League har guda uku.

Jose Mourinho, ya horas da Eto'o ne a karon farko a shekarar 2009 zuwa 2010, a Inter Milan inda suka lashe dukkanin kofunan da kulob din ta buga a shekarar, da suka hada da Serie A, Italian Cup, da kuma na zakarun turai.

Haka kuma ya horas da shi a kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake kasar Ingila.

Tsohon kocin yace abin mamaki ne in aka tuno cewa Samuel Eto'o bai taba lashe Ballon d'Or ba duk da irin bajintar da ya yi a harkar wasansa, ya ci kwallaye da dama kuma ya samu nasarori a lig daban-daban.

Ya kuma zama dan wasan gaba mafi kyau a duniya tsawon shekaru, saboda haka ina ganin ya dace ya lashe Ballon d'Or inji Mourinho.

A bangaren Afirka kuma Samuel Eto'o, ya lashe kyautar gwarzon dan
kwallon Afirka sau hudu, kuma ya zama na uku a kyautar hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA World Player a 2005) wanda aka daina bayarwa a yanzu.

Eto'o ya fafata wasannin sa a kungiyoyi 13 a kasashe 6 kuma ya samu nasarar jefa wa kasarsa ta Kamaru kwallo 56 a wasa 118.