Babu Tabbaci Ko Burtaniya Zata Amince Da Shugabancin Boris

Firai ministan Burtaniya Boris Johnson, na kokarin wanke siyasar sa, tun bayan hukuncin kotun kolin kasar da ta yanke hukunci jiya Tala, da cewar bukatar shi ta a dakatar da majalisar kasar ya sabawa dokokin kasar.

Hukuncin na nuni da cewar ‘yan-majalisaun, zasu koma bakin aiki a yau Laraba, ana kuma cigaba da kara kiran Firai ministan da yayi murabus. Burtaniyar dai zata fice daga jerin kasashen kungiyar turai a ranar 31 ga watan Oktoba, amma wannan ikirarin na Brexit don ficewa ya kara shiga cikin rudani.

Alkalan kotun 11 duk sun amince da hukuncin batare da hamayya ba, akan yunkurin Johnson, suka kuma kira hukunci da cewa “Hukunci na bakin iyakar karfin gwamnati”

“Matakin baiwa Sarauniya shawarar ta dakatar da majalisar, zai iya hana ‘yan majalisaun gabatar da ayyukan su kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar” a cewar babbar alkalin kotun Brenda Hale jiya Talata.