Masana a fannin tattalin arziki a Najeriya suna ta tsokaci kan halin kuncin rayuwa da aka shiga a kasar, inda wasunsu ke cewa wannan gwamnati mai ci ba ta da laifi. A 'yan kwanakin nan an samu wasu da suka yi zanga zanga nuna halin kuncin da aka shiga a kasar
WASHINGTON D.C. —
Ko da ya wasu masana tattalin arzikin na cewa wasu tsare-tsaren gwamnatin ne ba su da inganci.
A kashi na biyu na shirin Dimokradiya wani masanin tattalin arziki ya lissafa dalilai da suka sa ba za'a dorawa Shugaba Buhari laifin halin da kasar ke ciki ba yau.
Shugabannin baya su ne suka yi halin bera tare da yin watanda da arzikin kasa, su ne kuma ya kamata 'yan Najeriya su dorawa alhakin halin kunci da suke ciki yau.
Ga shirin Dimokradiya.
Your browser doesn’t support HTML5