Babu Kasar Duniya Da Aka Ci Amanarta Kamar Najeriya-Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari dake neman wa’adin mulki na biyu karkashin tutar Jam’iya mai mulki APC, ya bayyana cewa, babu kasa a duniya da aka ci amanarta kamar Najeriya, idan aka yi la’akari da abinda shugabannin gwamnatocin shekaru goma sha shida da suka shige suka yi.

A cikin hirarshi da Sashen Hausa, shugaba Buhari yace wanda yake gani sheri ne ko kuma bita da kulli gwamnatinsa ke yi wa gwamnatin da ta gabace shi, yaje turai yaga yadda ake cinikin mai da kuma kudaden da ake samu, daga nan ya bayyana inda kudin su ke.Shugaba Buhari ya bayyana cewa, gwamnatinsa bata iske komi ba a kasa.

Dangane kuma da kasafin kudin da ya gabatar gaban majalisa, shugaba Buhari yace, kasafin kudin shekara ta dubu biyu da goma sha tara da gwamnatinsa ta gabatar ya maida hankali a kan batun hanyoyi, da tsaro, da biyan ma’aika da kuma samar da wutar lantarki. Bisa ga cewarsa, kasar China ta amince zata yi wadansu hanyoyin mota da hanyoyin jirgin kasa, da dam-dam na Mambila, karkashin yarjejeniyar da aka kulla na biyan kashi goma sha biyar bisa dari na kudin da ake bukata, yayinda Najeriya zata biya sauran bashin cikin shekaru ishirin da ruwa kadan, Yace idan aka gaza samun tonon mai kamar yadda aka zata sai a sake duba hanyoyin da za a bi domin cike gibin da aka samu.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, yawanci basusukan da gwamnatinsa take biya ba ita ta ciwo su ba, ta gajesu ne daga gwamnatin da ta gabata.

A nashi bayanin, dan takarar jam’iyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana raunin yadda gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari take tafiyar da tsarin canjin kudaden kasashen ketare, Yace babu dalilin da za a ce farashin canjin kudaden ketare yana da matakai hudu ko biyar, inda za a ce wani ya saya dari uku, wani dari uku da biyar, wani dari uku da goma da dai sauransu. Bisa ga cewarshi, kamata ya yi farashin sayar da kudaden ya zama daya domin karfafa ‘yan kasuwa da masu zuba jari.

A fannin harkokin noma kuma Alhaji Atiku ya bayyana cewa an sami koma baya kasancewa har yanzu farashin kayan masarufi yana da tsada sosai, yayinda rashin tsaro ya hana manoma zuwa gona. Yace idan shine shugaban kasa, abu na farko da zai yi shine, taimakawa manoma ta wajen koyawa masu dabarun noma na zamani da basu rance.

Alhaji Atiku yace babu gaskiya a harsashen gwamnati na inganta harkokin noma kasancewa ba a gani a kasa ba,

Dangane kuma da batun cin hanci da rashawa, dan takarar jam’iyar PDP yace kage kawai ake mashi, ya kuma kalubalanci duk wanda yake zarginshi da cin hanci da rashawa ya kawo shaida. Idan kuma har ana ta ita a kama shi. Yace gwamnatin Buhari bata iya kama shi ba sabili da bata da shaida.

Saurari wannan bangaren hirar da Aliyu Mustapha ya yi da ‘yan takarar manyan jam’iyun siyasar Najeriya, Shugaba mai ci, Janar Muhammadu Buhari na jam’iyar APC, da kuma dan takarar babban jam’iyar hamayya PDP tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar Wazirin Adamawa.

Your browser doesn’t support HTML5

Hira da Buhari da Atiku PT3-12:00"