Manajan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger, ya bayyana cewa yana nan daram babu inda za shi, har ma yana cewa kwadayinsa na cimma wani abu a kulob din a yanzu, ya fi na lokacin da ya fara zuwa shekaru 20 da suka shige.
Arsene Wenger, dan asalin kasar Faransa, yana kara fuskantar matsin lamba a filin wasa na Emirates a saboda alamu sun fara nuna cewa Arsenal ba zata tabuka wani abin kirki ba a wannan kakar kwallo, kuma yiwuwar samun wani kofi ma tana raguwa.
A cikin ‘yan makonnin nan, magoya bayan Arsenal su kan shiga filin wasa da kwalayen dake yin kira ga manajan mai shekaru 66 da haihuwa da ya tattara nasa ya nasa ya bar kulob din, amma Wenger y ace babu inda za shi.
Manajan na Arsenal, yana da sauran shekara guda a kwantarakinsa. Yace bay a da shakka a game da kwadayinsa na bunkasa kulob din, yana mai cewa shi ya gina Arsenal ta hanyar aiki tukuru, ba tare da taimako daga waje ba.
Y ace idan aka dubi yadda Arsenal take a lokacin da ya zo shi kulob din da kuma yanzu, za a ga gagarumin ci gaban da aka samu, kuma yayi haka ne ba tare da taimakon wani ba.