Majalisar dattawan Najeriya tace sai ta tabbatar da cewa anyi amfani da kashi hamsin cikin dari daga cikin kasafin kudin shekara ta 2017, sannan zata gudanar da wani aiki akan kasafin kudin shekarar 2018, da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya kai wa majalisar kasar.
Shugaban kwamitin labarai na Majalisar dattawa Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ne ya tabbatar da hakan a wata hira da wakilin muryar Amurka, Mustapha Nasiru Batsari, a garin Minna. Yace Majalisar ba zata yi garaje ba akan kasafin kudin shekarar 2018.
Ya kara da cewa ganin lokacin da aka kawo kasafin kudi zuwa Majalisa da kuma abubuwa da yakamata ayi akai zai yi yuwa a samu da sauri kamar yadda mutane ke dauka.
Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, yayi Karin haske akan dalilin da yasa Majalisar kasar ta amince da bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari, na karbo bashin dalar Amurka, miliyan dubu biyu da miliyan dari biyar, yana mai cewa rancen wani bangare ne na rancen da aka sa a cikin kasafin kudi na shekara 2017, domin tabbatar da cigaba da aikin gwamnati.
Your browser doesn’t support HTML5