Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Unai Emery, ya ce abune mai wahala kungiyarsa ta iya lashe gasar firimiya na shekarar 2019/20, wanda za’a fara a watan Agusta mai kamawa, saboda yadda yaga saura kungiyoyin sun shiryawa gasar fiye da irin shirin da Arsenal ta yi.
Babban burin kungiyar ta Arsenal shine lashe kofin firimiya, ko kuma su samu kansu a cikin manyan kungiyoyi hudun farko a gasar firimiyar, domin samun damar buga kofin zakarun turai UEFA Champions League 2019/20.
Domin a kakar wasan data gabata ta 2018/19 Arsenal ta karane a mataki na biyar, wanda hakan ya hanata samun damar zuwa gasar zakarun turai.
Kocin yace ya zamo dole mu gayawa kanmu gaskiya, domin tazarar da take tsakaninmu da kungiyoyin Liverpool, Manchester City tanada yawa, saboda haka abinda ya kamata muyi shine cike wannan gurbi da yake tsakaninmu.
Ya kara da cewar kungiyar Tottenham taje wasan karshe na kofin zakarun turai, amman duk da haka yanzu ta kara karfin 'yan wasa, ita kuma Chelsea ta rike ‘yan wasanta in banda Hazard da ta sayar dashi ga Real Madrid kungiyar Manchester United kuma ta fisu shiri mai kyau domin irin 'yan wasan da ta ke nema da wadanda ta saya.
Unai Emery, yace ya zamo dole a kara 'yan wasa a Arsenal, matukar ana son burin kungiyar ya cika, Arsenal dai ta ware fam miliyan 45, wajen zawarcin 'yan wasa a yanzu haka, inda suke neman dan wasan Crystal Palace Wilfried Zaha, sai dai dan wasan zai iya kaiwa fam miliyan 80, kamar yadda kungiyarsa ta ke bukata daga duk kulob din da ke son sa.