WASHINGTON, DC —
Yayin da suka kawo ziyarar aiki Amurka abokin aiki Sahabo Aliyu Imam ya samu ya zanta da gwamnan jihar Neja Dr Babangida Aliyu Muazu kan abubuwa da yawa da suka shafi Najeriya.
A kan rabon kudin Najeriya yace sun je kasar Jamus su ga yadda suke rabawa jihohinsu kudin kasar. Yace yadda suke rabon suna lura ne da jama'a lamarin da ya banbanta da yadda Najeriya keyi. Yace ba wai domin ana samun abu a wurinka ba zaka fi kowa arziki ba. Wato kamar yadda wadanda suke da man fetur suke hakikancewa sai an basu kudin kacokan ko kuma rabi.
Gwamnan ya yi misali da irin rashin adalcin dake tafe da rabon kudin Najeriya. Yace a yi misali da kasafin kudin shekarar 2014 na jihohin kasar. Yace a duk jihohin arewa babu jihar da kason kudinta ya kai biliyan dari biyu da hamsin. Amma a kudancin Najeriya akwai jihohi masu biliyan dari uku ko biliyan dari hudu. Don haka irin wannan rabon bai zo daidai ba tamkar babu adalci a ciki. Abu na biye da wannan yawancin jihohin kudu dake samun kudi da yawa basu da mutane da yawa.
Dr Babangida yace sun sha yin wadannan maganganun. Najeriya ta dubi yadda Jamus keyi. Yace idan wata jiha ta samu kudi da yawa sai an yanke a tabbatar kowace jiha ta samu daidai kudin da zata iya aiki kafin wata jihar ta samu kari.
Batun cewa jihohin arewa sun zama kaska gwamnan yace maganar banza ce domin kafin
su zama kaska ai akwai wata kaskar. Ma'ana, da can kafin a samo man fetur ai da arzikin arewa a ka yi anfani dashi aka gano man fetur aka kuma hakoshi. Yace idan aka ce kuna kasa guda kamar kuna gida guda ne.
Dole alummomin kasar su zauna su tattauna domin a fahimci juna domin babu wani yankin kasar da zai ce shi ya tafi shi kadai. Duk wanda yake tsammanin zai iya raba Najeriya to kusan yana hauka ne.
Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5