Babbar Kotun Nijar Zata Yanke Hukunci Ga Masu Laifuffuka 50

Babbar kotun Shari'a ta Damagaram ta fara zaman shari'ar ta da ta saba yi ko wace shekara, duk da ma shekara biyu bata gudanar da shi ba sanadiyar rashi jagororirn kotun da aka samu.

A wannan zama za a duba manyan laifuka guda hamsin da suka shafi mutane tamanin da bakwai, da suka hada kisan kai na taron dangi, manyan barayi shidda, wata mata data sanya ma mijin ta gishirin lalle a abinci, da wata da ta kashe jaririn ta, sai kuma yawanci laifufukan na fyade ne.

A cewar mai gabatar da shari'a a kotun ta Damagaram, Salisu Shaibu, babban abin da ya fi daukar hankalin shari'ar ta bana, shi ne yawan fyaden da aka samu, fiye da shekarun baya, wanda duka yara ne da ba su wuce shekaru 13 ba, wanda shaye-shaye ya taimaka wajen yawaitar laifufukan.

Sabanin shekarun baya, a wannan karon shari'o'in zasu kai wata guda ana yin su, saboda cunkosa a gidan kaso, haka kuma kotun ta ce lalle a duba a dauki tsatsauran matakai da hukunci mai tsanani ga masu laifi.

Akwai bukatar dukan gawa don mai rai ya ji tsoro, biyo bayan yadda ake kyale mutane suna abinda suka ga dama shi yasa ake wasu laifufukan.

Ga rahoton Tamar Abari wakiliyar muryar Amurka daga Damagaram.

Your browser doesn’t support HTML5

Babbar Kotun Nijar Zata Yanke Hukunci Ga Masu Laifi 2'40"