KANO, NIGERIA -Hakan na zuwa ne kwana guda bayan wani rukuni na shugabanin Jam’iyyar ta APC daga mazabar ta Ganduje sun fito sun ayyana masu dakatarwar a matsayin ‘yayan APC na bogi.
Yau laraba aka ayyana cewa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, tsohon gwamnan Kano kuma shugaban Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya zai bayyana a gaban babbar kotun Kanon tare da iyalan sa, domin amsa wasu tuhumce tuhumcen zargin rashawa da cin hanci da gwmnatin jihar Kano ta Jam’iyyar NNPP ke yi masu.
Sai dai gabanin kotun ta zauna, kwatsam sai aka samu bullar wata oda da ita wannan kotun ta bayar wacce ke tabbatar da dakata da Dr Ganduje daga APC kamar yadda Haladu Gwanjo da wani mai suna Laminu Sani Barguma suka nema.
A hirar shi da Muryar Amurka, Barrister Ibrahim Sa’ad Kura lauyan masu shigar da karar yace, “sun nemi kotu ta tabbatar da cewa, dakatarwar da suka yi halastacciya ce”
To amma a zantawa da manema labarai a shalkwatar Jam’iyyar APC a Abuja yayin ziyara ga tsohon gwamnan na Kano a yau laraba, Alhaji Haladu Gwanjo wanda daya daga cikin mutane biyun da Barrister Ibrahim Sa’ad Kura ke magana a madadin su ya bayyana cewa, bashi da masaniya a kan wannan karar a matsayinsa na "lastaccen mai bada shawara ga Jam’iyyar APC na mazabar Ganduje a karamar hukumar Dawakin Tofa jihar Kano," ya ce, "ni a Abuja na kwana, ban san zancen zuwa kotu ba, wani na gani , ban kai kara ba kuma abin da akai min zan dauki matakin shari’a.”
A bangaren karar zargin cin hanci da rashawa da gwamnatin Kano ke yiwa tsohon gwamnan kuwa, lauyoyin bangarorin biyu sun tafka mahawara, kan rashin mika takardun tuhuma ko sammaci hannu da hannu ga Abdullahi Umar Ganduje, kamar yadda doka tace, al’amarin daya sa bai bayyana a zauren kotun ba.
Da yake tsokaci kan batun, Farfesa Kamilu Sani Fagge dake koyar da ilimin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero Kano kuma guda cikin masu fashin baki akan harkokin demokaradiyya da shugabanci ya ya bayyana cewa, “Wadannan abubuwa abin da suke nunawa shine, ita siyasar Kano ta koma ta gaba tsakanin bangarori daban daban musamman, tsakanin Gandujiyya da Kwankwasiyya kuma hakan zai kara tabarbara siyasar Kano ya kawar da hankalin gwamnatin daga yiwa Jama’a aiki.”
Tuni dai babbar kotun ta Kano, ta ayyana ranar 29 ga wannan wata na Afrilu a matsayin ranar da lauyoyin bangarorin biyu zasu bayyana domin amincewa da sigar gabatar da sammacin kotun kan batun zargin cin hanci da rashawa da gwamnatin Kano ke yiwa tsohon gwamna AbdullahI Umar Ganduje.
Saurari cikakken rahoto daga Mahmud Ibrahim Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5