Daraktan sashen Afirka na Muryar Amurka, Mr. Negussie Mengesha, wanda yayi tattaki zuwa birnin Abuja, shine ya jagoranci raba na’urorin aiki gangariya irin na zamani ga daukacin wakilan sashen Hausa dake sassa dabam dabam a fadin Najeriya.
Biyo bayan samar da kayan aikin da ake ji da su a duniya, Shin ko me shugabannin Muryar Amurka ke sa rai, Mr. Negussie Mengesha, yace “Abinda na ke sa rai shine duk lokacin da zaku samo rahoto, to ba kadai a rediyo ba, har ma da talabijin da hotuna, wannan sune a kalla abinda muke sa rai daga kowanne wakili.
Ya ci gaba da cewa Najeriya akwai dinbin labarun da ke faruwa a kullum, ba kawai labarun tashin hankali ko na Boko Haram ba akwai sauran labaru na ci gaba suma suna da matukar muhimmanci a gare mu.
Shima daya daga cikin turawan dake bayar da wannan horo Nicolas Pinot, yace wadannan kayayyakin aiki irin na zamani musamman wayar iphone na bada damar dauko labari a tace a kuma aika dashi nan take.
Muryar Amurka ta tashi daga matsayin rediyo kawai ta shiga layin sauran kafofin watsa labarai masu amfani da hanyoyi daban daban na zamani wajen watsa labarai ga mutane inji babban editan Sashen Hausa, Aliyu Mustaphan Sokoto. Wanda ya kare bayanin sa da cewa wannan wani yunkuri ne da gidan rediyon yake na ganin cewa yana kan gaba a fagen watsa labarai.
Your browser doesn’t support HTML5