Babban Sufeto Ya Kafa Kwamitin Sasanta Kananan Kabilun Najeriya

tambarin kasar Najeriya

Babban sufeton 'yan Sandan Najeriya Suleiman Abba ne ya kaddamar da kwamitin a Abuja

Yawan koke-koken da ake samu daga kananan kabilun Najeriya, da rigingimun Fulani makiyaya da abokan zaman su manoma sun sa babban sufeton 'yan sandan Najeriya Sulaiman Abba ya kaddamar da wani kwamitin da zai gano dalilan irin wadannan matsaloli da suka hada da sace-sacen dabbobi da sauran rigingimun dake kawo asarar rayukan jama'a, da kuma samar da hanyoyin warware su. An kafa wannan kwamiti ne ana sauran wani dan lokaci a shiga zabe gadan-gadan a kasar Najeriya.

Ga Madina Dauda da karin bayani daga birnin Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

Babban Sufeton 'yan sanda ya kafa kwamitin warware rigingimu a Najeriya.- 2':21"

Babban sufeton 'yan sandan na Najeriya Suleiman Abba ya kaddamar da wannan kwamitin ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta ware zunzurutun kudi har Naira miliyan dubu dari domin samar da dazuzzukan kiwo ga Fulani Makiyaya.

Kwamitin ya kunshi jami'an 'yan sanda daga shiyoyi shida na kasar Najeriya.