Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Ya Fusata da Yadda Ake Yawan Sace Mutane da Jami’ansa a Najeriya

IBRAHIM K. IDRIS, babban sifeton 'yansandan Najeriya

Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya ya fusata da yadda ake satar jama’a da ma jami’an ‘yan sanda, lamarin da ya kira abun kunya wanda ba zai amince da shi ba

Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya ya kira taron duk ilahirin kwamishanoninsa da na jihohin Najeriya 36 inda ya nuna fushinsa akan yadda ake yawan sace jami’ansa a kwannakin nan.

A jawabinsa ga kwamishanonin, Alhaji Ibrahim Idris, ya nuna bacin ransa inda ya ce su da suka kasance jami’an tsaro su ne kuma ake sacewa, lamarin da ya kira abun kunya.

Da ya juya kan kwamishanan jihar Neja inda aka sace babban jami’in dake kula da karamar hukumar Muya a garin Sarkin Pawa, Babban Sufeton ya ce jami’an ‘yan sanda na tafiya a hanyoyi galala suna barin bata-gari suna ci musu mutunci, har su dinga sace su. Yace haka ma aka sace mataimakin kwamishanan ‘yan sandan jihar Zamfara, abun da ya ce ba zai amince dashi ba.

A sharhin da ya bayyana kan wannan lamarin, Dr Kabiru Danladi Lawanti na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria ya ce abubuwa yanzu sun tabarbare fiye da yadda ake zato. Yana cewa akwai abubuwan da suka shafi talauci da rashin sanin inda aka sa gaba kuma kamata ya yi a yi nazari kan abubuwan dake faruwa domin shawo kansu.

Hassan Maina Kaina na da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Babban Sifeton ‘Yan Sandan Najeriya Ya Fusata da Yadda Ake Sace Mutane da Jami’ansa a Najeriya -2' 19"