Babban Jami'in Dan Sanda, 'Yan Shi'a Sun Rasa Rayukansu a Arangamar Abuja

Sheik El-Zakzaky

Wata arangama da ta kaure tsakanin ‘yan Shi'a da jami'an 'yan sandan Najeriya a birnin Abuja a yau Litinin ta yi sanadin mutuwar mukaddashin kwamishinan ‘yan sanda DCP Usman Umar.

Rahotanni sun ce an harbi jami'in dan sandan ne inda daga baya a ya cika a asibiti.

Haka nan ‘yan sandan sun ce wasu jami’ai masu matsayin mataimakan Sufuritenda biyu sun samu raunuka hade da wani wakilin gidan talabijin na Channels.

‘Yan Shi’an almajiran Ibrahim El Zakzaky sun ce an kashe masu fiye da mutum 20 a zanga-zanga mai zafi da su ka gudanar a Abuja.

Zanga-zangar dai da ta faro daga unguwar Maitama, ta samu cikas a daf da ma’aikatar harkokin waje inda ‘yan sanda suka tare hanya don hana ‘yan Shi’an wucewa, wanda hakan ya haddasa dauki ba dadi tsakanin sassan biyu da har a ka bankawa motocin kota-kwana na hukumar agajin gaggawa ta NEMA wuta.

Kakakin almajiran Elzakzaky da ke Abuja, Muhammad Ibrahim Gamawa, ya ce ba za su dakatar da muzaharar ba har sai an sako shugaban na su.

Fadar gwamnatin Najeriya a makon jiya ta bukaci ‘yan Shi’an su bi kadun El Zakzaky a kotu da ke Kaduna maimakon tayar da fitina a Abuja.

Mai taimakawa shugaban Najeriya kan labaru Garba Shehu ya ce ba zai yi wu shugaba Buhari ya ba da umurnin sakin wanda a ke tuhuma ba.

Tun farkon lamarin inji Garba Shehu, gwamnati na kaucewa irin wannan fitinar ce ya sanya ta ajiye El Zakzaky a waje mai ma’ana.

Rundunar ‘yan sandan ta bakin kakakin ta Frank Mba ta ce ta kama ‘yan Shi’an 54 kuma za ta gurfanar da su gaban kotu da zarar ta kammala bincike.

Babban sufeton na ‘yan sanda Muhammad Adamu ya ba da kashedin karshe kan abin da rundunar ta zayyana da bijirewa doka da ‘yan Shi’an ke yi.