Babban hafsan sojojin Najeriya shi ya sake bude wannan hanya mai mahimmanci ga kasashen Najeriya da Kamaru da Chadi da Afirka ta Tsakiya.
Jiya ce ranar tunawa da sojojin Najeriya kuma a ranar ce aka sake bude hanyar. Bayan ya bude hanyar sai Janar Buratai, babban hafsan sojojin Najeriya ya yi tattaki zuwa Dikuwa.
A Dikuwa Janar Buratai ya ga yadda alamura ke tafiya har ya taimaka wurin bada magunguna ga wasu mutanen dake jinya a asibiti. Yace hanyar nada mahimmanci sosai musamman ga jihar Borno akan harkokin kasuwanci.
Janar Buratai yace idan za'a tuna hanyar ce ta farko da sojoji suka fara kwatowa saboda mahimmancinta. Yace akan hanyar ce aka yiwa tawagarsa kwantan bauna har suka rasa soja guda kana wasu kuma suka jikata saboda haka su kansu 'yan ta'adan sun san mahimmancin hanyar. 'Yan ta'adan suna son su rike hanyar ne domin su dinga zirga zirgansu daga dajin Sambisa zuwa yankin da kasashen waje, musamman a bangaren tafkin Chadi.
Janar Buratai ya sake jaddadawa jama'a cewa sojojin kasar zasu samar da tsaro akan hanyar. Yace sun samu wasu rahotanni masu tada hankali cewa wasu sun hada baki da sojoji suna karban kudi daga masu sufuri wai domin su rakasu daga Maiduguri zuwa Gamboru Ngala.
Babban hafsan yace dole ne masu wannan mugun halin su daina, idan kuma ba haka ba duk wanda aka kama, tabbas za'a hukumtashi.
Shi ma gwamnan jihar Kashim Shettima ya yabawa shugaban kasa Muhammad Buhari game da yunkurin da yake yi na kawo karshen ta'adanci a jihar da ma wasu jihohin arewa inda 'yan ta'adan sukan addabi jama'a.
Gwamna Shettima yace shekara daya da rabi a baya birnin Maiduguri ya kusa fadawa hannun 'yan ta'adan amma yanzu komi ya canza baki daya domin an soma samun zaman lafiya. Yace yanzu suna ganin da yaddar Allah ta'adanci ya kawo karshe. Yace yanzu sojojin Najeriya sun kwato duk wuraren da 'yan Boko Haram suka mamaye da.
Yayinda aka bude hanyar motoci fiye da dari biyu suka yi jerin gwano zasu je garuruwa daban daban dake kan hanyar. Cikin shekaru ukun da hanyar bata biyuwa mutanen Gamboru Ngala idan sun taso daga Maiduguri sai sun shiga kasar Kamaru su zaga ta Yola da Gombe kafin su kai garinsu.
Ga karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5