Babban Daraktan kamfanin man Najeriya Dr. Maikanti Kachalla Baru ya kai ziyara fadar gwamnan Bauchi inda ya shaidawa gwmnan ya zo ne bisa ga umurnin shugaban kasa Muhammad Buhari kan binciken neman man fatur a jihar da makwafciyarta, wato Gombe.
Da yake magana da manema labarai yace ziyararsa cika umurnin shugaban kasa ne. Zasu bude aikin binciken karkashin kasa domin tabbatar cewa akwai man fetur a yankin da ya hada da Bauchi da Gombe. Yace zasu yi aiki a yankin da suke kira Gongola Basin da kuma tafkin Chadi. A yankin tafkin Chadi sun samu mai.
Gwamnan Bauchi Barrister Muhammad Abdullahi Abubakar ya bayyana irin taimakon da gwamnatinsa zata bayar domin gudanar da ayyukan. Yace sun yi alkawarin ba NNPC ofishi kyauta da kuma gidajen ma'aikatan da zasu turo jihar.
Sabanin abun da ya faru can baya gwamnan yace tunda yanzu shugaban kasa ne ya tasa keyarsu to ko shakka babu za'a cimma nasara.
Sanata Salisu Matori wanda yayi fice wajen ganin an soma aikin tono man fetur a arewa maso gabas ya dora alhakin jinkirin da aka samu akan rashin kulawar gwamnatocin da suka shude. Yace lokacin da kamfanin Rasha yayi aiki a yankinsu har za'a fara tono sai aka yi watsi da maganar.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5