Matakin, wanda ya fara aiki nan take, ya zo ne a matsayin martani ga rashin bin dokokin sashe na 12 (c), (f), (g), (h) na dokar Bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗi na shekarar 2020, kamar yadda aka bayyana a cikin wata sanarwa ta hanun Mukaddashin Daraktan Sadarwa na CBN, Sidi Ali Hakama.
Babban bankin na CBN ya nada sabbin shuwagabannin da za su jagoranci al’amuran wadannan cibiyoyin hada-hadar kudi, wanda hakan ke nuna aniyarsa na tabbatar da bin ka’ida da kuma kiyaye tsarin bangaren kudi a Najeriya.
Sanarwar ta bayyana sabbin shugabannin bankin Union da aka nada sun hada da Yetunde Oni, Manajan Darakta (MD) da babban jami’in gudanarwa (CEO) da Mannir Ubali Ringim, babban darakta. (ED).
Babban bankin na CBN ya ce Hassan Imam da Chioma Mang za su jagoranci harkokin bankin Keystone a matsayin shugaba da ED.
Babban bankin ya kuma bayyana Lawal Mudathir Omokayode Akintola da Chris Onyeka Ofikulu a matsayin Shugaba da ED na bankin Polaris.
Babban bankin ya jaddada cewa wadannan nade-naden za su fara aiki nan take.
Matakin rusa kwamitocin ya biyo bayan wasu laifuka daban-daban da bankunan suka tafka, da suka hada da rashin bin ka’ida, gazawar gudanar da harkokin kamfanoni, yin watsi da sharuddan lasisi, da kuma shiga ayyukan da ke barazana ga daidaiton harkokin kudi.
A kokarin da CBN ya yi na magance matsalolin da kan tasowa, ya gayyaci shugabannin gudanarwa da shugabannin bankunan da abin ya shafa zuwa wani taro a ranar 10 ga watan Janairu. Wasu gwamnoni uku, sun yi jawabi a hukumance ga shugabannin bankunan, inda suka bayyana matsalolin rashin bin ka’ida da sauran laifuffuka kafin a sallami shugabannin hukumomin a hukumance.
Wannan mataki na CBN ya biyo bayan rade-radin da ake yi a baya-bayan nan game da yiwuwar karbe bankunan, sakamakon wani rahoto daga babban mai bincike na CBN, Jim Obazee, wanda bincikensa ke da alaka da tsohon shugaban bankin Godwin Emefiele.
Babban bankin ya yi watsi da wadannan hasashe, inda ya tabbatar da masu ajiya da amincin kudadensu.
A baya dai mai binciken na musamman ya gayyaci shugaban bankin Titan Trust Bank (TTB) Babatunde Lemo da wasu masu hannun jari biyu kan sayan bankin Union, inda ya bankado wasu kura-kurai da cece-kuce da aka samu a kan cinikin.
Sabbin nade-naden da aka yi na zartaswa dai wani muhimmin matakai ne wajen sake fasalin wadannan cibiyoyin hada-hadar kudi a Najeriya, kuma hakan za’a iya cewa CBN na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da ingantaccen tsarin hada-hadar kudi a Najeriya.