Babban Bankin Amurka Ya Kara Kudin Ruwa

Shugaban Amurka Barack Obama

A karon farko cikin kusan shekaru 10, Jiya Laraba, babban bankin Amurka ya kara kudin ruwa kan rance da yake baiwa bankunan kasuwanci, shawarar da nan da nan ta kara ruwa kan basussuka da 'yan kasuwa da daidaikun jama'a zasu biya,lamari da zai shafi tattalin arzikin kasashe a fadin duniya.

Bayan watanni shugabannin babban bankin suna gudanar da shawarwari, sun kara kudin ruwan da kwata na kashi daya cikin dari, bayan da aka shafe shekaru bakwai ana kusan babu kudin ruwa kwata-kwata.

Mintoci da daukan wannan mataki,manyan bankunan Amurka suka kara kara kudin ruwa kan bashi da suke baiwa manyan baokan hulda dasu, mataki da zai kuma shafi wadanda zasu yi jingine gidajensu su karbi bashi daga hanun bankuna.

Ahalinda ake ciki kuma shugaba Obama ya sanya hanu kan dokar kasafin kudi na wucin gadi, gabannin amincewar da ake sa ran majalisun dokokin Amurka zasu yi yau Alhamis, kan kasafin kudi na dala milyan zambar domin shekara mai zuwa.