Adadin cinakayya da kuma tsadar kaya sun haura a watan Janairu a Amurka, al'amarin da ke nuna cewa ya kamata Babban Bankin Amurka ya kara kudin ruwa.
WASHINGTON DC —
Adadin cinakayyar ya karu ne cikin wata guda kawai. Wani masanin tattalin arziki da ke aiki da bankin PNC mai suna Gush Faucher ya ce cigaba da aka samun na da nasaba da sabbin ayyukan yi da su ka samu da kuma karin albashi yayin da aka shiga karancin ma'aikata
Masana tattalin arziki a Amurka kan yi nazarin adadin cinakyya saboda tattalin arzikin Amurka ya ta'allaka sosai ne kan yawan cinikin da ake yi a kasar.
Wani rahoto na dabam ma na nuna cewa farashin kaya sun yi haurawar da rabon da aka ga haka tun shekaru hudu da su ka gabata.