Sabon salon da zanga-zangar yaki da kuncin rayuwa da wasu matasan Najeriya ke yi ta hanyar daga tutar kasar Rasha na jan hankalin masana kimiyyar siyasa da diflomasiyya.
Wannan ya biyo bayan matsayar babban hafsan tsaro, Manjo Janar Christopher Musa, da ya zaiyana hakan da cin amanar kasa.
Duk da cewa Janar Musa, bayan ganawar hafsoshin tsaro da shugaba Tinubu, bai bayyana wadanda gwamnati ke zargi da daukar nauyin dinka tutocin ba, ya nuna soja ka iya shiga lamarin baya ga matakan ‘yan sanda.
Ganin matasa a Kano, Kaduna da wasu sassa dauke da tutar Rasha ya kawo neman bahasi inda a ka ji su na gayatar soja su karbe ragamar mulki.
Masanin kimiyyar siyasa a jami’ar Bayero Dokta Sa’idu Ahmad Dukawa ya bayyana nazarin da ya yi kan dalilan daga tutar, wanda ya ce a ciki har da kin jinin hukumar lamunin duniya IMF da bankin duniya da kuma lura da yanda wasu kasashen Afurka Ta Yamma su ka yi bayan juyin mulkin soja.
Shugaban gamayyar kungiyoyin arewa, Jamilu Aliyu Charanci, ya ba wa gwamnatin shawarar daukar matakan saukake rayuwa don rage wannan bore da ke zama tamkar gayyatar juyin juya hali.
Har ila yau Dokta Sa’idu Dukawa ya jaddada fifikon gano masu daukar nauyin samar da tutocin a maimakon dirar mikiya kan matasa, wadanda ba mamaki, ba su san girman matakin da su ka dauka ba.
Hakika dokar hana yawo a wasu daga jihohin da zanga-zanga ta shafa ta rage kaifin tunzurin, duk da matasa, musamman a Abuja, sun lashi takobin ci gaba har sai sun cika kwana 10.
Rahoton Nasiru Elhikaya, Abuja.